Hausa
/
2011
/
10
UTME
Objective
II
Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin biyu: daya ya yiwu an ci an koshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.
Kullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.
A al'adance, hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowaca rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da kosai ko kunu. Wasu kuma, sukan dumama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma danwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko kubewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai "Daidai ruwa daidai kurji."
Har ila yau, ko da yake ba kowa yake da karfin dora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami makwabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira makwabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga dan'uwansa.
A zamanin da, za a ga Bahaushe yana kokarin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.
Labarin ya na nuna cewa Bahuashe yakan yi noma domin
Answer:D
Practice more with TestDriller
Get TestDriller
To see detailed solution to this question and thousands of other questions offline, download TestDriller UTME. Practice rigorously for UTME, learn from video and text materials, enjoy educational games, summary of JAMB literature books, compete with your peers, win prizes and more.
