UTME past questions
Hausa / 2011 / 1
UTME Objective

I
A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi kokarin ganin ya yi ilmin boko dana Arabiya. Bayan Salihi ya kammala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare. Domin an ce "Ilimi gishirin zaman duniya."
Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Dahira dadi ba, don bata son danta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne dansu tilo namiji, sauran hudun kuwa duk mata ne. Bugu da kari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin wadannan makarantu.

Bayan Salihi ya isa makaranta, sai ya dukufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka kulla abota da wani dan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata kungiyar asiri.


Da ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi kokarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. "In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka" in ji abokinsa.

Ganin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa kungiyar, in ya so komai ta tafasa to kone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami'an tsaro suka kamo dukkan 'yan kungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun. Da ma an ce, "Komai nisan jifa kasa za ya fado."


Mece ce dangantakar Salihi da Dahira?
A
Wa da kanwa
B
Uba da 'ya
C
Miji da mata
D
Da da Uwa
Answer:D
Practice more with TestDriller

To see detailed solution to this question and thousands of other questions offline, download TestDriller UTME. Practice rigorously for UTME, learn from video and text materials, enjoy educational games, summary of JAMB literature books, compete with your peers, win prizes and more.

Get TestDriller