Hausa
/
2010
/
9
UTME
Objective
"Ba neman aure ke da wuya ba, shiga-ka-fito." ka ga shiga-ka-fito din nan, lallai shiga-ka-fito din ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al'ada ta tanada, wadanda dole sai an haye su, suna da yawa.
yanzu dauki misalin kayan na-gani-ina-so, wato 'yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma'anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin aren 'yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da 'yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?
Gangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kudi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar. Ina, ko kadan!
Kada ka mance da kudin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa rannar biki. Kudi ne madiddiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.
Duk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karaka ina ke nan daga wannan gari zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi. I, za su san shi mana, tun da ba kawo jiki kma, uwa-uba za a Shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.
Hakika duk wadannan abubuwa al'ada ce kawai ta kakaba wa al'umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can karshen sahu!
Zi kau a labarin na nufin
Answer:B
Practice more with TestDriller
Get TestDriller
To see detailed solution to this question and thousands of other questions offline, download TestDriller UTME. Practice rigorously for UTME, learn from video and text materials, enjoy educational games, summary of JAMB literature books, compete with your peers, win prizes and more.
