UTME past questions
Hausa / 2010 / 5
UTME Objective

A karanta wadannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu
I
A karkar da ma wasu manyan garuruwa kalilan, mutane kan hadu su rika cin abinci tare. Akan zabi gidan mutum daya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zabi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala so sai zuwa gidan, musamman da damina.

A wurin haduwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka kware suke shan yabo da godiya. Wadanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al'amari ya yi muni ke nan.

Cikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da dan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin wadannan nau'o'in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganra da irin cefanen da maigida ya yi.

Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. wanda ma ba ya da karfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.


Babar fa'idar cin abinci tare, ita ce
A
sada zumunci tsakanin mutane
B
yalwar abinci daban-daban
C
sa mata su kara himma
D
wani zai yi santi da abincin wani
Answer:A
Practice more with TestDriller

To see detailed solution to this question and thousands of other questions offline, download TestDriller UTME. Practice rigorously for UTME, learn from video and text materials, enjoy educational games, summary of JAMB literature books, compete with your peers, win prizes and more.

Get TestDriller